Isa ga babban shafi
Amurka

Obama ya kammala ziyara a Afrika

Shugaban Amurka Barack Obama ya kammala ziyarar da ya kai a kasashen Kenya da Habasha a Afrika yayin da ya fice daga birnin Addis Ababa a marecen jiya talata zuwa Washington.

Obama  ya kasance shugaban Amurka na farko da ya gabatar da jawabi a gaban Kungiyar  AU.
Obama ya kasance shugaban Amurka na farko da ya gabatar da jawabi a gaban Kungiyar AU. REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Obama shi ne Shugaban Amurka na farko da ya kai ziyara Kasar Kenya da ta kasance tushen mahaifinsa wanda kuma ya gabatar da jawabi a zauren Kungiyar Tarayyar Afrika a Habasha.

Ajawabin da ya gabatar a taron kungiyar Tarayyar Afrika a birnin Addis Ababa shugaba Obama ya yi allawadai da shugabannin kasashen Afrika da ke makalewa kan karagar mulki.

Obama ya kasance shugaban Amurka na farko da ya gabatar da jawabi a gaban Kungiyar AU.

Obama ya bukaci yaki da cin hanci da rashawa a nahiyar Afrika, tare da yin kira ga sauran kasashen duniya su sauya yanayin huldarsu da Afrika ta hanyar habbaka harkokin kasuwanci tsakaninsu.

Shugaba ya jinjinawa dakarun wanzar da zaman lafiya na Kungiyar Tarayyar Afrika, yana mai cewa kasarsa ta tsaya tsayin daka domin yaki da ta’addaci da sauran tashe tsashen hankula a kasashen na afrika.

Obama ya bukaci tabbatar da tsarin mulkin demokradiyya da da bai wa al’umma cikakken ‘yanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.