Isa ga babban shafi
Nijar-Masar

An kashe dogarin ofishin jekadancin Nijar a Masar

Wasu ‘Yan bindiga sun harbe wani Dan sandan Masar da ke gadin ofishin jekadancin Nijar a birnin Al Kahira da dare a ranar Talata, ‘Yan sanda sun ce ‘Yan bindigar sun tsere bayan sun harbi Mai gadin.

Masar na fama da hare hare tun hambarar da Morsi
Masar na fama da hare hare tun hambarar da Morsi REUTERS/Mohamed Abd El Ghany
Talla

‘Yan sandan sun ce mutane biyu ne suka kai harin a saman Babur inda suka kuma raunana wani Dan sanda bayan sun kashe guda a ofishin jekadancin Nijar da ke kudu maso yammacin birnin Al Kahira.

Babu dai wata kungiya da ta fito ta yi ikirarin kai harin.

Tun dai lokacin da aka hambarar da gwamnatin ‘yan uwa musulmi ta Mohammed Morsi a 2013, kasar Masar ke fama da hare hare daga kungiyoyin mayaka masu da’awar jihadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.