Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram: Ziyarar Buhari a Kamaru

A yau Laraba shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kai ziyarar aiki a kasar Kamaru, daya daga cikin makwabciyar Najeriya da ke fama da rikicin Boko Haram.

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari statehouse
Talla

Mai magana da yawun shugaba Buhari Femi Adesina, ya bayyana a wata sanarwa cewa shugaban zai tattauna da takwaransa na Kamaru Paul Biya kan batutuwa da dama musamman ma matsalar Boko haram.

Masana na ganin wannan dama ce ta dakile ayyukan Boko Haram da ke addabar arewacin kasashen biyu.

Dr Haruna Yerima masani harkokin tsaro, ya ce mayakan Boko Haram na tsallakawa zuwa Kamaru idan sun yi barna a Najeriya, don haka Buhari zai nemi hadin kan mahukuntan Kamaru don murkushe mayakan.

Shugaba Buhari zai kai ziyarar a Kamaru tare da rakiyar gwamnoni jihohi shida na kasar, da babban sakatare a ma’aikatar tsaron kasar da shugaban hukumar tara bayanan sirri na kasar.

Gwamnonin jihohin dai sun hada da Adamawa da Akwa Ibom da Benue da Borno da Cross Rivers da kuma Taraba, wadanda dukkaninsu sun yi iyaka da kasar Kamaru.

Bayan ganawa da shugaban Paul Biya, Muhammadu Buhari zai kuma gana da ‘yan Najeriya da ke zaune a jamhuriyar Kamaru, kafin daga bisani ya wuce zuwa Jamhuriyar Benin domin gudanar da ziyarar aiki ta yini daya a ranar Asabar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.