Isa ga babban shafi
Najeriya-Kamaru

Shugaba Buhari zai gana da Paul Biya na Kamaru

A gobe laraba shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kai ziyarar aiki a kasar Kamaru, daya daga cikin kasashen makobtan Najeriya sannan kuma take fama da ayyukan Boko Haram.

Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari REUTERS
Talla

Mai magana da yawun shugaba Buhari Femi Adesina, ya bayyana a wata sanarwa cewa shugaban zai tattauna da takwaransa na Kamaru Paul Biya kan batutuwa da dama musamman ma matsalar Boko haram.

Bayan rantsar da shi akan karagar mulki ranar 29 ga watan Mayun da ya gabata, Muhammadu Buhari ya ziyarci jamhuriyar Nijar kafin daga bisani ya wuce zuwa kasar Chadi, kuma tun a wannan lokaci ne ake hasashen cewa zai kai ziyara a kasar ta Kamaru.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.