Isa ga babban shafi
Amurka -Kenya-Ethiopia

Obama ya gargadi shugabannin da ke makalewa kan karagar mulki

Shugaba Barack Obama dake ziyarar aiki a Afrika a yayin jawabin da ya gabatar a gaban taron kungiyar Tarayyar Afrika a birnin Adis Ababa na Kasar Habasha, Ya yi Allah-wadai da Shugabannin Kasashen Afrika dake kin sauka daga karagar Mulki.

Obama na jawabi a zauren kungiyar Tarrayar Afrika
Obama na jawabi a zauren kungiyar Tarrayar Afrika REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Shugaba Obama dai ya fito karara a jawabinsa inda ya soki zarcewa da mulki da shugabanin ke yi ko da wa’adin mulkin su ya cika.

Shugaba Obama ya kuma bukaci shugabanin da su inganta Demokradiya ta hanayar barin al’umma suna bayyana ra’ayin su ba tare da fuskantar tsangwama daga gwamnatoci ba.

Ya kuma tabo batutuwa da suka shafi tauye hakkin dan’adam da suka kun shi kama ‘yan jaridu da wasu masu fafutukar kare hakkin jama’a.

Batun cin hanci da rashawa da yanzu haka ya gurgunta tattalin arzikin kasashen Afrika na daga cikin batutuwan da shugaba Obama ya yi jawabi akai tare da yin kira ga shugabanin na daukar matakai domin magance su.

Ziyarar ta shugaban Amurka Barack Hussein Obama ya kasance ziyarar farko a kasar sa ta asali Kenya kuma jawabi na farko na wani shugaban Amurka a taron kungiyar Tarrayar Afrika.
 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.