Isa ga babban shafi
Kenya-Habasha-Amurka

Ziyarar Obama a Habasha da Kenya

Shugaban kasar Amurka Barack Obama, ya isa birnin Addis Ababa na kasar Habasha a marecen jiya lahadi domin gudanar da ziyarar aiki, bayan da ya share tsawon kwanaki biyu a kasar Kenya.

Shugaban Amurka Barack Obama yana ziyara a Habasha
Shugaban Amurka Barack Obama yana ziyara a Habasha REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Obama wanda ya sami gagarumin tarbo daga al’ummar Habasha cikinsu har da Firaminista Hailemariam Desalegn, a nan gaba zai gana da hukumomin kasar ta Habasha, kuma kamar dai yadda majiyoyi ke cewa, zai tabo batun rikicin da ake fama da shi a Sudan ta Kudu, kafin ya gabatar da jawabi a zauren kungiyar Tarayyar Afirka da ke birnin na Addis Ababa.

Kafin ya isa Habasha, Obama ya fara zuwa kasar Kenya ne, inda ya tabo batutuwa da dama da suka shafi kasar da kuma alakar Amurka da nahiyar Afirka

A ranar Lahadi ne Shugaba Obama ya kammala ziyara a Kenya tushen iyayensa, kuma a ziyarar shugaban ya bukaci sauyi a Kenya ta bangaren cin hanci da rashawa da rikice rikecen kabilanci da matsalar yi wa mata kaciya.

Mr Obama kuma ya bukaci sauyi a fannin siyasar Kenya, ta hanyar yin watsi da kabilanci tare da yin kira a kara karfafawa mata guiwa, sabanin yadda aka mayar da mata baya a Kenya.

Sannan batun tsaro da baranar mayakan Al Shabaab na cikin batutuwan da suka mamaye ziyarar Obama a Kenya, kuma ziyarar ta taimaka wajen inganta huldar Amurka da Kenya a fannin tsaro da tattalin arziki.

Baya ga wannan kuma Obama ya yi kira ga mahukuntan Kenya su mutunta ‘yancin addini musamman musulmi da ba su da yawa a kasar.

Amma a bangaren auren jinsi, shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ya jaddada wa Obama cewa auren abin la’anta ne a kasarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.