Isa ga babban shafi
Nijar

Kotu ta cire wa Mahamane Ousmane rigar kariya a Nijar

Babbar kotu a kasar Jamhuriyyar Nijar ta sanar da cire wa tsohon shugaban kasa Alhaji Mahamane Ousmane rigar kariya domin amsa tambayoyi a kotu.

Tsohon shugaban Nijar Muhamane Ousmane
Tsohon shugaban Nijar Muhamane Ousmane abamako.com
Talla

Bayanai sun ce ana zargi Ousmane da kuma sauran shugabannin jam’iyyun adawa na kasar ne da nunawa kotun rashin da’a bayan da suka wallafa wani kundi mai nuna rashin amincewa da wasu daga cikin hukunce-hukuncen da kotu ke yankewa da suka shafi takaddama tsakanin gwamanati da ‘yan adawa.

Tsohon shugaban dai Yana cikin manyan ‘Yan siyasa da ke adawa da babbar kotun kasa a Nijar.

Jina Abdoullaye wani na hannun daman Mohamane Ousmane, ya danganta matakin da siyasa yana mai zargin gwamnati da yin amfani da iko domin karya ‘yan adawa tare da hanawa duk wani da ake ganin zai  shiga takarar zaben shugaban kasa anan gaba.

Mahamane Ousmane dai shi ne shugaban dimokuradiya na farko da aka zaba a Jamhuriyyar Nijar, kuma shugaba na hudu a kasar, wanda ya yi zamanin mulkinsa a 1993 kafin sojoji su kifar da gwamnatinsa a 1996.

Tun hambarar da gwamnatinsa ya ke ci gaba da neman kujerar shugabancin Nijar a Jam’iyyar CDS Rahama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.