Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram-Kamaru

Mutane da dama sun mutu a harin da aka kai Damaturu da Kamaru

Wani harin kunar bakin wake da wata mata mai tabin hankali ta kai cikin kasuwan a garin damaturu na jihar Yobe a tarayyar Najeriya ya kashe akalla mutane 14 tare da jikata wasu 47.

Harin yankin Maroua,na kasar Kamaru
Harin yankin Maroua,na kasar Kamaru AFP PHOTO/STRINGER
Talla

Rahotannin dai sun ce a bisa al’ada yau ce ranar kasuwace a yankin da harin ya auku da safiyar yau lahadi.

Wani dan kasuwa kuma shaida gani da ido Garba Abdullahi ya shaida wa kamfanin dilanci labaran Farasna cewa matar da ta kai harin  sananiya ce a kasuwa domin ta jima dauke da ciwon tabin hankali kuma akalla za ta kai kimanin shekaru 40 a duniya.

Harin dai na zuwa ne adai-dai lokacin da rahotannin daga kasar kamaru ke cewa mutane 20 sun rasa rayukansu bayan harin kunar bakin wake da wata yarin itama dai ta kai a wani mashaya da ke garin Maroua na arewacin kasar

Wannan lamari dai na zuwa ne, kwanaki kalilan bayan wani tagwayen hare-hare bama-bamai da ya yi ajali mutane kasar da dama.

Majiyoyin sun tabbatar da cewa an kai harin kamaru ne a daran jiya Assabar idan matafiye dare ke zama, kuma akalla akwai wasu 79 da suka samu munanar rauninka.

An dai dauran alhakin wannan harin ne kan mayakan Boko Haram da ke Najeriya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.