Isa ga babban shafi
Burundi

‘Yan adawa sun bukaci a sake zabe a Burundi

Wani shugaban ‘yan adawa kasar Burundi, wanda ya tsaya takara da Pierre Nkurunziza, Agathon Rwasa ya kalubalanci sakamakon zaben da aka gudanar wanda ya baiwa Pierre Nukurunziza nasara kara zarcewa a wani wa’adi na uku.

Zaben da ya baiwa Nkurunziza Nasara
Zaben da ya baiwa Nkurunziza Nasara REUTERS/Mike Hutchings
Talla

Rwasa ya ce tilas akwai bukatar sake gudanar da wannan zaben.

Rwasa wanda ya samun yawan kuri’ur kashi 18.9 cikin 100, ya jadada cewa idan har aka ki amince da batun sake zabe to akwai yiwuwar samun rabuwar kawuna a gwamnatin kasar.

Wannan dai na zuwa ne adai-dai loakcin da shugaban kasar Amurka da ke ziyarar a kasar Kenya ya ce babu adalci a zaben Burundi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.