Isa ga babban shafi
Amurka-Kenya

Obama ya gabatar da batun auren jinsi guda a Afrika

A ziyarar sa ta kwanaki 2 a Kasar Kenya da zai kai shi har zuwa kasar Habasaha Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya yi kira da a baiwa masu ra’ayin auren jinsi guda yancinsu.

Shugaban Kasar Amurka, Barack Obama da Uhuru Kenyatta na Kenya
Shugaban Kasar Amurka, Barack Obama da Uhuru Kenyatta na Kenya REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Obama dai ya dangatan bukatar ta shi ne da irin kalubalin da ya fuskanta a Amurka wajen amincewa da wannan tsarin.

Obama dai ya ce yana gani cewa akwai bukatar baiwa kowa na sa daman a rayuwa a bisa tsari da doka, don haka nuna wa mutane da ke da burin auren jinsu guda wariya a Afrika kamar an tauye musu haki ne da batun  yanci dan Adam.

Sai dai kuma Shugaba kasar kenya Uhuru kenyatta da ke karba bakwanci Obama a yanzu haka bai tankawa wannan batu ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.