Isa ga babban shafi
Gambia

Jammeh ya yi wa Fursunoni da dama afuwa a Gambia

Shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh ya yi wa mutane da dama da ke daure a gidan yari afuwa cikinsu har da wadanda aka yankewa hukuncin kisa, don murnar cikar shekaru 21 da darewarsa karagar mulkin kasar.

Shugaban Gambia Yahya Jammeh
Shugaban Gambia Yahya Jammeh AFP PHOTO / SEYLLOU
Talla

Sai dai wannan afuwa ba ta shafi wadanda aka kama bayan da suka yi yunkurin kifar da gwamnatinsa ba a cikin watan Disambar bara, yayin da tsohon babban kwamandan askarawan kasar Janar Lang Tombong wanda aka sama da laifin cin amanar kasa a shekara ta 2010 da wasu mutane 7 za su ci moriyar wannan afuwa wadanda suka nemi kifar da gwamnatin shugaban a 2006.

A watan Maris ne aka yanke wa Sojojin hukuncin kisa wasu kuma hukuncin daurin rai da rai bayan kama su da laifun yunkurin juyin mulki.

Tun a 1994 Jammeh ke shugabanci a Gambia wanda ya dare kan madafan ikon kasar ta hanyar juyin mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.