Isa ga babban shafi
Najeriya

Sai watan Satumba Buhari zai nada Ministoci

Jaridar Washington Post ta jiyo shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ke ziyara a Amurka na cewa ba zai nada ministoci ba sai zuwa watan Satumba mai zuwa. Shugaba Buhari ya ce idan har ya nada ministocin a cikin watan satumba, ba ya nufin cewa an makara domin hakan ta faru da Obama.

Shugaban Amurka Barack Obama na ganawa da Muhammadu Buhari na Najeriya
Shugaban Amurka Barack Obama na ganawa da Muhammadu Buhari na Najeriya REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Shugaban ya bayar da misali da shugaban Amurka Obama, a wa’adin mulkinsa na farko inda sai da ya share tsawon watanni ba tare da ya nada wasu daga cikin mukamai a majalisarsa ta ministoci ba.

Buhari ya ce kawai bukatar a gina tubalin shugabanci nagari domin kaucewa kura-kuran da gwamnatocin baya suka fuskanta.

A cikin sakonsa na Sallah ga 'Yan Najeriya, shugaba Buhari ya bukaci 'Yan Najeriya su sa hakuri domin yana aiki tukuru domin tabbatar da canjin da da suka zaba.

00:59

Hon Faruk Adamu Aliyu

A ziyararsa a Amurka, Buhari ya  ce rashin gina tabbatar da shugabanci nagari tun da farko shi ke sa shugabanni na samun matsala a Najeriya.

Shugaban na Najeriya ya jaddada matsayinsa na kawo karshen cin hanci da rashawa a Najeriya tare da inganta tattalin arzikin kasar.

Sannan Buhari ya nemi taimakon shugaban Amurka Barack Obama na kwato wa Najeriya kudadenta dala biliyan 150 da aka sace aka ajiye a kasashen waje.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.