Isa ga babban shafi
Masar

Omar sharif Jarumin fina finai na Masar ya rasu

Shahararen Jarumin wasan fina finan nan na duniya dan kasar Masar Omar Sharif, da ya zama tauraro a fagen wasanin cinema a duniya sakamakon rawar da ya taka a cikin fina finan "Lawrence d'Arabie" da kuma "Docteur Jivago", ya rasu a yau juma’a a birnin kairo na kasar Masar sakamakon tsayawar bugun zuciyar da ya hadu da shi yana dan shekaru 83 a duniya

Omar Sharif na Masar
Omar Sharif na Masar AFP PHOTO / Damien Meyer
Talla

Omar Sharif ya rasu ne a tsakiyar ranar yau juma’a sakamakon haduwa da bugun zuciya a birnin Al-kahira.

An kwantar da shi a wani kwararen asibiti dake kula da masu fama da cutar 'Alzheimer" ta karkarwar jiki, kamar yadda abokin aikinsa dan kasar Britaniya Steve Kenis yaa sanar wa kamfanin dillacin labaran Faransa na AFP.

Kafin mutuwarsa dai an bayyana cewa Koshin lafiyarsa ta tabarbare ta yadda baya iya cin abonci da kuma shan ruwa.

Rashin lafiya dai ta tilastawa marigayi Sharif kauracewa fagen fina finai tun cikin 2012, bayan fitowarsa a fim din "Rock The Casbah", na Laïla Marrakchi, fim din da ya zama na karshe daga cikin fina finai 70 da yayi a rayuwarsa.

Omar Sharif Ya fara sana’arsa fina finai ne, a karkashin daraktan nan mai shirya fina finai dan kasar Masar Youssef Chahine, wanda a 1954 ya saka shi a cikin fim dinsa mai sunan "Ciel d'enfer". Amma kuma tauraronsa ya haska ne a duniyar fina finai a fim din "Lawrence d'Arabie" da aka shirya a (1962), wanda ya bashi damar sabe kambion Golden Globe na kwararen mataimakin jarumi a wannan lokaci.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.