Isa ga babban shafi
Burundi

Nkurunziza ya kauracewa taron Burundi a Tanzania

Shugaban Burundi Pierre Nkurunziza ya kauracewa taron shugabannin kasashen gabashin Afrika da ke kokarin sansata rikicin kasar a yau Litinin a birnin Dar es Salam na Tanzania.

Shugaban Burundi Pierre Nkurunziza
Shugaban Burundi Pierre Nkurunziza AFP/Carl de Souza
Talla

Shugaban ba zai halarci taron ba a cewar kakakinsa.

Ana ganin Nkurunziza ya kauracewa taron ne domin ci gaba da yakin neman zabensa wa’adi na uku, matakin da ya haifar da rikici a Burundi.

An shafe makwanni ‘Yan adawa na gudanar da zanga-zangar adawa da matakin Nkurunziza na neman wa’adin shugabanci na uku.

Sama da mutane 70 suka mutu a zanga-zangar da aka shafe watanni biyu ana yi a sassan Burundi, yayinda da kusan mutane 150,000 suka fice kasar zuwa makwabta.

Yanzu haka Gwamnatin Nkurunziza ta ki amincewa da Jakadan da Majalisar Dinkin Duniya ta aika kasar Abdoulaye Bathily saboda yadda ta soki zaben ‘Yan Majalisun kasar da aka yi makon jiya.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewar zaben ‘Yan majalisu an gudanar da shi ne ba tare da inganci ba tare da hana wa ‘yan jaridu sa ido akai.

Kasar Amurka ta nemi a dage zaben shugaban kasa a Burundi har sai mahukuntan kasar sun samar da hurumin da za a gudanar da karbabben zabe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.