Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Dakarun Salva kir sun fatataki yan Tawaye

A wani farmaki da suka fara tun jiya lahadi zuwa yau Sojojin sudan ta kudu sun sanar da kwace ikon yankin Malakal dake arewa maso gabashin kasar daga hannu ‘yan tawayen masu goyon bayan tsohon mataimakin shugaba Riekck Machar.Mutane da dama ne suka samu rauni,yayi da  aka samu asarar rayyuka  bangarorin biyu.

Salva Kiir Shugaban kasar Sudan ta kudu
Salva Kiir Shugaban kasar Sudan ta kudu Reuters/Goran Tomasevic
Talla

A cikin watan da ya gabata ne garin Malakal ya fada a hannu ‘yan tawayen kuma yana daya daga cikin yankuna da Sudan ta kudu ta dokara da su wajen fitar da danyan man fetur.

 A yan watani da suka gabata dai ne Gwamnatin kasar Sudan ta Kudu ta ce, za ta hukunta duk Sojan da aka samu da hannu wajen yi wa Mata fyade, jinjirar kasar dake fama da yakin Basasa, kamar yadda wani rahoton Majalisar dinkin duniya ya sanar.
Ma su bincike na tawagar Majalisar Dinkin Duniya a kasar Sudan ta kudu sun bayyana gano aikata kazaman laifukan cin zarafin dan adam da sojojin gwamnatin kasar ta Sudan ta Kudu ke aikata a kasar.
Rahoton ya dogara ne kan bayanan da sheidu 115 da abin ya shafa suka bayar, da kuma shaidun da Majalisar Dinkin Duniya ta tattara daga yankunan da aka aikata wannan mummunan cin zarafin matan da kuma fararen hula a kasar da yaki ya daidaita.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.