Isa ga babban shafi
Cote D'Ivoire

Bambanta ra'ayin game da sabuwar dokar yaki da ta'addanci a Ivory Coast

Kungiyoyin kare hakkin bil’adama da kuma ‘yan adawa a Cote D’Ivoire, sun bayyana fargabarsu a game da sabuwar dokar fada da ayyukan ta’addancin da aka kafa a kasar, kwanaki kadan bayan da kungiyar Ansr Dine ta yi barazanar kai hare-hare a cikin kasar mai makotaka da Mali.

Shugaban Cote D'Ivoire, Alassane Ouattara.
Shugaban Cote D'Ivoire, Alassane Ouattara. REUTERS/Thierry Gouegnon
Talla

A karkashin wannan doka dai, jami’an tsaro na damar kaddamar da bincike akan duk wanda ake zargi da ta’addanci ko kuma gudanar da bincike a gidansa, yayin da dokar ta bai wa jami’an tsaro damar kwacewa ko sauraren sakonnin wadanda ake zargi.

Har ila yau dokar ta bai wa jami’an tsaro damar tsare mutum har tsawon kwanaki 8 kafin gurfanar da shi a gaban alkali, abin da ‘yan adawa ke zargin cewa zai iya kasancewa makami ga gwamnatin kasar domin tursasawa jama ‘a a lokacin zaben da ake shirin gudanarwar a kasar cikin shekarar bana.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.