Isa ga babban shafi
Najeriya

Dan kunar bakin wake ya kashe mutane 6 a cocin Potiskum

A Najeriya wani dan kunar bakin wake ya kai hari tare da kashe mutane akalla 6 a wata mujami’a da ke wajen birnin Potiskum na jihar Yobe a daidai lokacin da masu ibada ke gudanar da addu’o’i a yau lahadi.

Awani harin da Boko Haram ta kai a Potiskum shekara ta 2015
Awani harin da Boko Haram ta kai a Potiskum shekara ta 2015 AFP PHOTO / AMINU ABUBAKAR
Talla

Rahotanni sun ce maharin ya shiga cocin ne da ke unguwar Jigawa a garin na Potiskum, inda nan take ya fasa bam din da yake dauke da shi, kuma daga cikin wadanda suka rasa rayukansu har da daya daga cikin fastocin da ke jagorantar addu’o’in.

Shaidu sun ce ko baya ga wadanda suka rayukansu akwai wasu mutane da dama da suka sami raunuka a cikin wannan coci da ake kan ginawa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.