Bensouda na binciken kisan fararen hula a birnin Conakry
Yau asabar babbar mai shigar da kara ta kotun duniya Fatou Bensouda za ta kammala ziyarar da take gudanarwa a birnin Conakry na kasar Guinee, inda kotun ke gudanar da bincike a game da kisan da sojojin kasar suka yi wa fararen hula 157 a ranar 28 ga watan satumbar shekara ta 2009.
Wallafawa ranar:
A watan okotobar bara ne ya kamata Bensouda da kuma sauran masu bincike daga kotun su kasance a birnin Conakry, to sai dai sakamakon bullar cutar Ebola a kasar sai a dage wannan ziyara.
Binciken ya zo ne a daidai lokacin da tsohon shugaban gwamnatin mulkin sojan kasar wanda a lokacin mulkinsa ne aka aikata wannan kisa Keftin Moussa Dadis Camara ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a zaben shugabancin kasar da za a gudanar a watan oktoban bana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu