Mutane 6 sun mutu a rikicin Burundi
Akalla mutane shida aka kashe cikin su har da Dan Sanda guda a ci gaba da tashin hankalin da ake samu a kasar Burundi inda al’ummar ke dakon sakamakon zaben ‘Yan Majalisun da aka gudanar a kasar.
Wallafawa ranar:
Rahotanni sun ce fada ya barke ne a unguwar Cibitoke da ke birnin Bujumbura, wanda ya ke sansanin ‘Yan adawa ne ma su adawa da takarar shugaban kasa Pierre Mkurunziza.
Amma ‘Yan Sanda sun ce rikicin ya barke ne tsakanin kungiyoyin ‘yan bindiga.
Mutane sama da 70 suka rasa rayukansu a rikicin siyasar kasar da aka kwashe watanni biyu ana yi, yayin da kuma kusan mutane 150,000 suka tsallaka zuwa makwabtan kasashe saboda fargabar barkewar yakin basasa.
Rikicin siyasa dai ya barke ne a Burundi bayan da shugaban kasar Pierre Nkurunziza ya bayyana aniyarsa ta neman wa’adin shugabanci na uku.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu