Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotun Kano ta hanawa EFCC cafke Kwankwaso

Kotun Jihar Kano ta dakatar da hukumar EFCC cafke Tsohon gwamnan Jihar Sanata Rabiu Kwankwaso wanda ya rufe kansa a gida tsawon kwanaki biyu, Kotun kuma ta dage sauraren karar gwamnan tsakanin shi da ‘Yan Fansho da ke kalubalantarsa akan kudadensu da ya wawushe.

Tsohon Gwamnan Kano Senata Rabiu Musa Kwankwaso
Tsohon Gwamnan Kano Senata Rabiu Musa Kwankwaso pointblanknews.
Talla

Wakilin RFI Hausa Abubakar Isa Dandago wanda ya halarci zaman Kotun a garin Gezawa ya ce kotun ta dage sauraren karar har zuwa 15 ga watan Yuli.

Dandago ya ce Mai shari’a Muhammad Yahya ya haramtawa EFCC kame Kwankwaso har sai kotun ta kammala bincikenta.

A zama na gaba, Kotu za ta gayyaci EFCC domin sauraren karar.

Kotun ta ce ba zata yi aiki da jita-jita ba har sai abinda sakamakon bincikenta ya tabbatar.

‘Yan Fansho ne dai suka nemi Hukumar EFCC ta kame Kwankwaso domin kalubalantar kudadensu da Tsohon Gwamnan ya yi amfani da su wajen gudanar da ayyuka a zamanin shugabancinsa a Kano.

Kwankwaso kuma ya ruga kotun Kano ne domin hanawa EFCC ta cafke shi.

Yanzu haka sabuwar gwamnatin Ganduje ta gaji bashin kudi da aka bayyana sun kai sama da Naira Biliyan 370.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.