Isa ga babban shafi
Mali-MDD

An kashe Sojoji Majalisar dinkin duniya a Mali

A wani kazamin harin da ta kai sansani Soji dake arewacin Mali, Kungiyar al-Qaeda ta kashe dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar dinkin duniya shida tsakanin garin Timbuktu da Goundam.

Sojin Mali a fagen daga
Sojin Mali a fagen daga AFP/PHILIPPE DESMAZES
Talla

Majiyoyin kasar sun ce an aikata kisa ne da Misalin karfe 9 na safe agoggon GMT kuma bayan  sojojin da suka rasa rayukansu,  akwai wasu biyar da aka jikata.

Wannan dai ba shine karon farko da ake kai harin kan dakarun dake aikin wanzar da zaman lafiya a Mali ba.

Majalisar dinkin duniya ta ce daga lokacin da rundunar ta suka fara aiki a kasar cikin shekara ta 2013 kawo yanzu ta yi asarar sojoji 35.

Tuni dai sakatare Janar na majalisar Ban ki-Moon ya yi allawadai da kisan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.