Isa ga babban shafi
Najeriya

"A ba Matan da ‘Yan Boko Haram suka yi wa Fyade damar zubar da ciki"

Majalisar Dinkin Duniya ta roki hukumomin Najeriya su ba Matan da ‘Yan Boko Haram suka yi wa Fyade damar zubar da ciki da suke dauke da shi bayan an ceto su daga hannun Mayakan. Majalisar na ganin ya kamata a ba su damar zubar da cikin domin sauwaka wa rayuwa, lura da halin da mayakan suka jefa su.

Wasu 'Yan Matan Chibok sun tsere daga hannun Boko Haram
Wasu 'Yan Matan Chibok sun tsere daga hannun Boko Haram AFP PHOTO/STR
Talla

Zeid Ra’ad Al Hussein, kwamishinan jinkai na Majalisar ya ce wasu daga cikin matan na bukatar zubar da cikin, amma suna tsoro.

A cikin wani rahoto da ta fitar, Kungiyar Kare hakkin Bil’adama ta Amnesty International tace sama da Mata da ‘Yan Mata 2,000 Mayakan Boko Haram suka sace tun a 2014 hadi da ‘Yan Matan Makarantar garin Chibok 276 da aka yi garkuwa da su.

Jami’in na Majalisar Dinkin Duniya Zeid ya ce an ci zarafin Matan ta hanyar fyade da auren dole. Kuma yawancinsu da dama suna dauke da Ciki wanda suke son rabuwa da shi.

A tsarin Najeriya Mace na iya zubar da ciki idan rayuwarta na cikin barazana, akan haka ne Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga mahukuntan kasar su amince a zubar wa Matan da ciki.

Dakta Emman Shehu na kungiyar BringBackOurGirls da ke fafutikar ganin an kubutar da ‘Yan Matan Chibok ya ce a bar Matan su yanke shawara ba tare da an tursasa ma su ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.