Isa ga babban shafi
Mali-Cote d'Ivoire-Mauritania

Mali: Ansar Dine ta yi barazanar kai hare hare a Cote d’Ivoire

Kungiyar Mayakan Ansar Dine da ke kasar Mali ta dauki alhakin kai hare haren da aka kai kusa da iyakar kasar wanda ya kashe sojoji uku da maharan guda Tara, tare da yin barazanar kaddamar da hare hare kasashen Mauritania da cote d’Ivoire.

Mayakan Ansar Dine na Mali
Mayakan Ansar Dine na Mali DR
Talla

Wani malami da ke Magana da yawun kungiyar Ismael Khalil ya ce babu tantama su suka kai harin garin Nara da Fakola a hirarsa da kamfanin dillancin labaran Faransa, inda ya ke cewar sun yi haka ne don horar da makiyan addinin Islama.

Khalil ya ce zasu zafafa hare hare kan kasashen da ke nuna kiyayya ga addinin Islama.

Tun a farkon shekarar nan ne mayakan suka fara kaddamar da hare hare a kan iyakokin Mali da Mauritania da Cote d’Ivoire bayan sun dade suna kai hare hare a arewacin Mali.

Wannan na zuwa ne a yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi barazanar daukar matakin sanya takunkumin kan duk wata kungiya a Mali da ta karya yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla.

‘Yan Tawayen kasar sun sanya hannu kan yarjejeniyar ce bayan an dauki dogon lokaci ana tafka mahawara a karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya.

Yanzu dai haka an girke sojojin Majalisar a fadin kasar ta Mali don tabbatar da zaman lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.