Isa ga babban shafi
Najeriya

INEC: Buhari ya nada Amina Zakari shugabar riko

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Amina Bala Zakari a matsayin shugabar Hukumar zaben kasar na riko sakamakon kawo karshen aikin wa’adin shugabancin Farfesa Attahiru Muhammad Jega na shekaru biyar a ranar Talata, 30 ga watan Yuni.

Farfesa Attahiru Jega ya fice INEC bayan wa'adinsa ya kawo karshe
Farfesa Attahiru Jega ya fice INEC bayan wa'adinsa ya kawo karshe newspotng.com
Talla

Shugaban Ma’aikata Danladi Kifasi ya ce shugabar rikon wadda da ma kwamishiniya ce a hukumar za ta rike mukamin har zuwa lokacin da zaa nada sabon shugaba na din din din.

Amina Zakari ta fito ne daga Jihar Jigawa shiyar arewa maso yammacin Najeriya. Kuma ta taba rike mukamin mai bai wa Shugaban kasa shawara a zamanin mulkin Cif Olusegun Obasanjo.

Farfesa Attahiru Jega shi ya jagoranci zaben 2011 da zaben 2015.

‘Yan Najeriya sun yaba wa Jega kan yadda ya gudanar da karbabben zabe a 2015 da kasashen duniya suka amince da shi.

Jega wanda tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya nada, ya farfado da darajar INEC ga idon ‘Yan Najeriya musamman sauye sauyen da ya samar da suka hada da samar da katin zabe na din din din da kuma na’urar tantance masu kada kuri’a.

Kafin ya fice INEC, Farfesa Jega ya mika ragamar tafiyar da hukumar zuwa ga Ambasada Mohammed Wali daya daga cikin kwamishinoni.

Amma daga baya Shugaban kasa ya nada Amina Bala Zakari a matsayin shugabar riko.

Ana sa ran Jega zai koma koyarwa a Jami’ar Bayero da ke Kano.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.