Isa ga babban shafi
Chadi

Sojojin Chadi sun cafke wani babban kwamanda Boko Haram

Ministan cikin gidan kasar Chadi Abderehim Biremi Hamid, ya ce jami’an tsaron kasar sun yi nasarar cafke babban kwamandan kungiyar Boko Haram da ke kula da kasar Chadi da kuma yankin arewacin kasar Kamaru.

Sojojin Chadi da ke yaki da Boko Haram.
Sojojin Chadi da ke yaki da Boko Haram. REUTERS/Emmanuel Braun
Talla

Abderehim Biremi ya Shaidawa RFI cewa, Bayan musayar wuta, a jiya litinin sojojin kasar sunyi nasara Cafke kwamandan tare da wasu muhimman takardu, da kuma layukan wayoyi na kasashe daban-daban.

Biremi ya ce baya ga shi akwai wasu mukarrabansa da suka cafke, kuma daya daga cikinsun ya bayyana inda suke hada bama-bamai.

Rahotannin sunce jami’an tsaron Chadi sun kai samame ne a gidan da Mayakan ke mafaka, yayin da biyar daga cikinsu nan ta ke suka fasa bama-baman da ke jikinsu.

Hakumomin Chadi sunce ‘yan ta’adda 6 ne suka mutum da’yan sanda 5 sannan kuma akwai wasu ‘yan sanda 3 da suka samu raunuka, amma dai rayukansu ba sa cikin hatsari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.