Isa ga babban shafi
Sudan

Dakarun kasar Sudan ta Kudu na kashe mata bayan yi masu fyade.

A wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a yau talata, ta zargi sojojin Sudan ta Kudu da aikata miyagun laifufuka da suka hada da kona mata bayan sun yi masu fiyade.

Sojojin gwamnatin Sudan ta Kudu.
Sojojin gwamnatin Sudan ta Kudu. REUTERS/James Akena
Talla

A cikin wannan sabon rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, ta bayyana yadda sojojin ke cin zarafi mata a wasu yankuna kasashen da ake fama da matsanancin fada tsakanin bangaren gwamnati da ‘Yan tawaye.

Majalisar tace Akan yi amfani da sigar cin zarafi da dama akan matan, a wasu lokuta ma hadda garwashi domin tirsasa musu bayyana inda 'Yan tawaye suke.

Majalisar ta zargi 'yan tawayen da fyade da kisa da kuma daukar yara kanana aiki.

Rahotan ya kara da cewar, akwai wasu mata 9, da sojojin suka yiwa fyade, wasu daga cikin su matan aure ne inda suke musu fyaden a gaban ‘ya’yansu.
Rikicin Sudan Ta Kudu dai na ci gaba bayan kasa cimma yarjejeniyar samun zaman lafiya a tsakanin shugaba Salva Kiir da tsohon mataimakin sa Rieck Machar, Mutane sama da dubu uku ne suka rasa rayukan su sakamakon rikicin, yayin da sama da miliyan daya da rabi suka tsere daga kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.