An bukaci a biya diyan mahakan Ma’adanai a Marikana
Iyalan mahaka ma’adanan karkashin kasa da Jami’an ‘yan Sanda suka yi wa kisan kiyashi a garin Marikana na Kasar Afrika ta kudu sun bukaci gwamanati ta biya su diya bayan wani bincike da aka gudanar.
Wallafawa ranar:
Kisan kiyashin na garin marikana daya yi sanadiyar mutuwar mahaka ma’adinan karkashin kasa 34, ya faru ne a shekara ta 2012 yayin da iyalansu da wadanda aka raunata a harin suka bukaci gwamanati ta biya su diya, kamar yadda lawyan da ya tsaya musu mai suna Dali Mpofu ya bayyana.
Lauyan ya ce zai shigar da kara a kotu game da wannan batun kafin sake zagoyawar ranar tunawa da aukuwar lamarin karo na uku.
An dai danganta wannan kisan a matasyin mafi muni tun bayan kawo karshen mulkin wariyar launin fata a kasar Afrika ta kudu shekaru 20 da suka gabata.
Lauyan da ke wakiltan mutane 300 a kan wannan batun ya bayyana cewa, ya zama dole a shigar da karar kafin ranar 16 ga watan Agustan wannan Shekarar.
Tuni dai iyalan mamatan da wadanda aka jikata suka bayyana bacin ransu, saboda wanke manyan jami’an gwamanti da ake zarginsu da hannu a aikata laifin kisan yayin da kuma bincike ya nuna cewa kananan Jami’an 'yan sanda kawai ne ke da laifi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu