Boko Haram : Buhari zai kai ziyara Kamaru bayan Azumi
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da goron gayyata da Shugaban Paul Biya ya aiko ma sa zuwa Kamaru domin tattauna batun rikicin Boko Haram. Buhari zai kai ziyarar ne bayan kammala Azumin Ramadan.
Wallafawa ranar:
Ofishin shugaban na Najeriya ya tabbatar da ziyarar Buhari zuwa Kamaru idan an kammala Azumin watan Ramadan.
Shugaba Paul Biya dai ya kauracewa taron kasashen da ke makwabtaka da Najeriya da aka gudanar a Abuja kan matsalar Boko Haram, lamarin da wasu ke ganin dangantaka ce da ta yi tsami tsakanin kasashen biyu wadanda suka shafe shekaru suna takaddama kan yankin Bakassi.
Kamaru da Nijar da Chadi sun taimaka wa Najeriya kwato garuruwa da dama da Mayakan Boko Haram suka kwace.
Kuma yanzu Najeriya da Kamaru da Chadi da Nigar da Benin sun amince su kafa runduna ta musamman domin yakar Boko Haram da ke barazana ga kasashen.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu