Yara 250,000 na fama da Yunwa a Sudan ta kudu
Majalisar Dinkin Duniya tace kimanin Yara kanana 250,000 na fama da matsalar karancin abinci sakamakon rikicin kasar da aka shafe watanni 18 ana gwabza fada tsakanin dakarun gwamnati da ‘Yan tawaye.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Majalisar Dinkin Duniya tace jiragen sama masu saukar Angulu sun kai kayan agaji ga dubban mutanen da ke tsere wa rikicin kasar.
An dai kai wannan dauki ne ga mutane 30,000 a Jihar Unity .
Rahotanni sun ce yanzu haka adadin mutanen da ke zama da yunwa a kasar sun kai sama da miliyan 4 da rabi, cikinsu har da yara kanana kimanin miliyan guda.
Rikicin Sudan ta kudu ya barke ne a watan Disamban 2013, bayan shugaban kasar Salva Kiir ya zargi tsohon mataimakinsa Riek Machar da yunkurin kifar da gwamnatinsa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu