Isa ga babban shafi
Tanzania

Migiro ta shiga takarar shugabancin Tanzania

Tsohuwar babbar jami’ar Majalisar Dinkin Duniya, Asha-Rose Migiro ta bayana aniyarta ta neman tikitin tsayawa takarar shugabancin Tanzania da za a gudanar a ranar 25 ga watan Oktoba mai zuwa.

Asha-Rose Migiro, Babbar Jami'ar Majalisar Dinkin Duniya
Asha-Rose Migiro, Babbar Jami'ar Majalisar Dinkin Duniya AFP / PIUS UTOMI EKPEI
Talla

Magiro ta bi sahun Mataimakin Shugaban kasa da Firaminista da wasu mutane 33 da suke neman tikicin tsayawa takarar shugaban kasa karkashin Jam’iyyar CCM mai mulki a kasar.

Ko wacece Asha Rose Migiro?

Asha Rose Migiro, tsohuwar mataimakiyyar Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ce, kuma an dai hafe ta ne a ranar 9 ga watan yulin shekara ta 1956 a garin Songea da ke yankin Ruvuma, bayan kammala karatun Firamare da Sakandare, ta ci gaba da karatu a Jami’ar Dar es Salam inda ta karbi digiri na farko da na biyu a fannin shari’a kafin daga bisani ta samu digiri na uku a jami’ar Konztanz da ke Kasar Jamus a shekara ta 1992.

Migiro ta karantar a jami’ar Dar es Salam kafin ta rike mukamin Ministar ci gaban al’umma da ministan harkokin waje.

Migiro ta taba kai ziyara Italiya a watan Satumban shekara ta 2009 inda ta tattauna da Fafaroma Benedict kan cin zarafin da ake yi wa mata.

Yanzu kuma ita ce mace ta hudu cikin mutane 36 da ke fafutikar neman titkitin tsayawa takarar shugabancin kasar Tanzania a karkashin inuwar jam’iyyar CCM mai mulki bayan ta bayyana aniyarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.