Isa ga babban shafi
Sudan-Afrika ta kudu-ICC

Shugaban kasar Sudan Umar Hasan Albashir ya koma gida daga kasar Afrika ta kudu

Shugaban kasar Sudan Umar Hasan Albashir ya koma gida daga kasar Afrika ta kudu, inda kotu ta bukaci gwamnatin kasar da ta hana masa komawa gida domin gurfanar da shi a gaban kotun duniya dake zargisa da aikata laifukan yaki a yankin Darfur kamar yadda ministan yada labaran kasar ta Sudan ya sanar.

Shugaban kasar Sudan Umar Hassan Al Bashir.
Shugaban kasar Sudan Umar Hassan Al Bashir. REUTERS/Mohamed Nureldin Abdallah
Talla

Ita dai kotun hukunta manyan laifufuka ta ICC ta bada umurnin kama shugaba Umar al Bashir ne a shekarar 2009 saboda tuhumar da take masa na laifufukan yaki da kuma kisan kare dangi, sai dai duk da wanann umurni shugaban ya ziyarci kasahse irin su Chadi, Kenya da Najeriya ba tare da fuskantar wata matsala ba.

Shugabanin kungiyar kasashen Afirka dai sun soki matsayin kotun ta Duniya dake bukatar kama shugaban, inda suke zarginta da zama wace ake anfani da ita wajen musgunawa shugabanin Afirka, ganin babu shugaban wata kasar Turai da ta taba gurfanarwa.

Firaministan Habasha Hailemariam Desalegn yace akwai gibi sosai akan yadda kotun ke gabatar da ayyukanta, tunda ta bari ana anfani da ita dan musgunawa yan Afirka, yayin da shugaba Yoweri Museveni na Uganda ya bayyana kotun a matsayin wani makamin Turawa.

Shi kuwa shugaban kasar Rwanda Paul Kagame cewa yayi kotun ta zama mai zaben wadda take so ta ciwa mutunci.

Shugabar gudanarwar kungiyar tarayyar kasahsen Afirka Nkosazana Dlamini Zuma ta soki bukatar kama shugaban na Sudan da ta danganta da cin fuska.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.