Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya amince da zaben Shugabannin Majalisu

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana goyan bayansa ga shugabanin Majalisun kasar da aka zaba duk da yake ya bayyana goyan bayan sa da matsayin jam’iyyar su ta PDP.Sai dai Jam’iyyar APC ta bayyana cewar ba ta amince da zaben ba.

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari. Reuters/Afolabi Sotunde
Talla

Sanarwar da mai bashi shawara kan harkokin yada labarai Femi Adeshina ya raba, ta tababtar da matsayin shugaban cewar a shirye ya ke ya yi aiki da duk wadanda Majalisar ta zaba.

A ranar Talata ne dai aka gudanar da zabukan shugaban majalisar dattijai wanda Sanata Bukola Saraki ya lashe, yayyin Yakubu Dogara ya yi nasara a majalisar wakilai.

Dukkannin shugabannin biyu dai sun kasance a baya 'yan jam'iyyar PDP amma daga bisani suka canja sheka zuwa Jam'iyyar APC sakamakon rikicin cikin gida da ya ki ci ya ki cinyewa.

Buhari dai ya ce ya so ace anyi amfani da tsarin da Jam'iyyar APC ta tanadar, amma dai duk da haka ya yaba da yadda aka gudanar da zaben akan tsari.

Sai dai APC ta yi watsi da zaben shugabannin Majalisar a cikin wata sanarwa da ta fitar a Jiya Talata.

Jam’iyyar ta ce ba da yawunta aka zabi Saraki da Dogara ba domin mambobinta ba su ra’ayin shugabancinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.