Isa ga babban shafi
Najeriya

Saraki ya zama shugaban Majalisar Dattijai

An zabi tsohon gwamnan Jihar Kwara Bukola Saraki a matsayin shugaban Majalisar Dattijan Najeriya karo na takwas, a yayin da kuma aka zabi Ike Ekweremadu na Jam’iyyar PDP a matsayin mataimakinsa.

Sabon Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya Tsohon Gwamnan Jihar Kwara Bukola Saraki
Sabon Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya Tsohon Gwamnan Jihar Kwara Bukola Saraki REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

An zabi Saraki ne ba hammaya bayan Tsohon gwamnan Zamfara Sanata Ahmed Sani Yariman Bakura ya gabatar da sunansa a matsayin dan takara, nan take ne kuma Sanata Dino Melaye na Jam’iyyar APC daga Jihar Kogi ya amince da shi.

Sanata Ekweremadu na PDP daga Jihar Enugu ya lashe zaben mataimakin shugaban Majalisar ne bayan ya doke Ali Ndume na PDP daga Jihar Borno.

Zaben majalisar dai ya kara fito da baraka a tsakanin mambobin Jam’iyyar APC mai mulki a Majalisar a yayin da aka gudanar da zaben ba tare da wasu ‘Yan majalisar ba.

Yanzu haka kuma ana ci gaba da gudanar da zaben Shugabannin Majalisar wakilai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.