Isa ga babban shafi
Najeriya

Mutane da dama sun mutu a harin Yola

Akalla mutane 31 aka tabbatar da mutuwarsu bayan da wani dan kunar bakin wake ya tayar da bom a wata babbar kasuwa da ke Jimeta a Jihar Adamawa arewacin Najeriya.Babban Jami’in Kungiyar Agajin gaggawa ta NEMA Sa’ad Bello ya ce sun samu gawarwakin mutane 31 da kuma 38 da ke kwance a gadon Asibiti.

Garin Minchika da Mayaka a Jihar Adamawa da Boko Haram suka kona
Garin Minchika da Mayaka a Jihar Adamawa da Boko Haram suka kona REUTERS/Akintunde Akinleye
Talla

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Adamawa tace bayan idar da Sallar Magariba a jiya Alhamis dan kunar bakin wake ya tayar da bom a kasuwar Fallujah a Jimeta.

Wannan na zuwa ne bayan an kai wani harin Bom a garin Maiduguri a jiya Alhamis inda wata budaddiyar mota da abkawa wani shingen bincike a kusa da barikin Sojoji.

Jerin hare haren na zuwa a yayin da sabon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke kammala ziyara a kasashen Nijar da Chadi kan yadda za a kawo karshen mayakan Boko Haram da ke addabar yankin arewa maso gabaci da kuma kasashen da ke kewaye da tabkin Chadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.