Isa ga babban shafi
Najeriya-Chadi

Buhari ya inganta hulda da Chadi da Nijar

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yaba da kokarin da hukumomin kasar Chadi da Nijar suka yi, na tallafawa a yakin da ake yi da kungiyar Boko Haram tare da inganta huldar kasashen da Najeriya domin kakkabe mayakan.

Mohammadu Buhari na Najeriya tare Mahamadou Issoufou na Nijar
Mohammadu Buhari na Najeriya tare Mahamadou Issoufou na Nijar AFP PHOTO / BOUREIMA HAMA
Talla

Buhari ya kai ziyara Nijar da Chadi inda ya tattauna da shugabannin kasashen game da neman hadin kansu don yaki da Boko Haram.

Buhari ya fara kai ziyara Nijar kafin ya mika zuwa Chadi.

Shugaba Buhari da ke magana a yayin ziyarar da ya kai wa shugaba Idriss Deby, ya nemi karin hadin kan hukumomin birnin N'Djamena a yakin da ake yi da ta’addanci a yankin.

Buhari wanda aka rantsar a ranar Juma’a ya sha alwashin kawo karshen ayyukan ta’addanci da aka shafe shekaru shida ana kashe mutane a arewa maso gabacin Najeriya.

Shugaban Chadi ya yi alkawalin ba Buhari hadin kai wajen yaki da Boko Haram tare da bayar da taimakon da ya dace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.