Gobara ta hallaka sama da mutane 90 a Ghana
Akalla sama da mutane 90 ne, suka rasa rayukansu sakamakon wata gobara da ta tashi a wani gidan mai da ke birinin Accra na kasar Ghana.Gobarar ta tashi ne a lokacin da ake tafka wani ruwa kamar da bakin kwarya wanda ya tilastawa mutane fakewa a gidan man.
Wallafawa ranar:
Gobarar data fara tun acikin daran jiya laraba a unguwar Kwame Nkrumah ta yadu har zuwa muhallin mutane da ke kusa da gidan man.
A lokacin daya kai ziyara inda lamarin ya auke Shugaban kasar Ghana John Dramani ya bayyana Gobarar a mastayin mumunar bala’i daya samu kasar.
Rahotanin dai na cewa adaddin mamata ka iya zarce adaddin da aka fitar a yanzu, kuma masu aikin ceto na ta kai kawo domin kwashe gawarwakin mutane da suka kone.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu