Isa ga babban shafi
Burundi-Amurka

An dage zaben majalisun dokokin kasar Burundi

Gwamnatin kasar Burundi tace an dage zaben ‘Yan Majalisun kasar da aka shirya yi gobe juma’a har sai wani lokaci nan gaba da hukumar zaben kasar zata sanar. Willy Nyamitwe, mai Magana da yawun shugaban kasar ya bayyana dage zaben, bayan ‘yan adawan kasar sun ce a shirye suke su koma tattaunawa dan warware rikicin siyasar kasar.A wani bangaren kuma, kasar Amurka ta bukaci shugabanin kasashen Afirka ta Gabas da su tura wakilai Burundi don jaddada matsayin su ga shugaba Pierre Nkurunziza, dake neman wa’adi na uku wajen ganin anyi zabe mai inganci.Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar John Kirby yace Amurka bata goyon bayan takarar shugaban, wanda ya sabawa yarjejeniyar zaman lafiyar da akayi a Arushan kasar Tanzaniya, don kawo karshen yakin basasar kasar da akayi a shekarar 2005.Matsayin shugaba Nkurunziza ya haifar da zanga zanga da kuma tashin hankalin da tuni ya lakume rayukan mutane sama da 30. 

Shugaban kasar Burundu Pierre Nkurunziza
Shugaban kasar Burundu Pierre Nkurunziza REUTERS/Jean Pierre Aime Harerimana
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.