Isa ga babban shafi
Sudan

An sake rantsar da Al Bashir na Sudan

Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir ya sake karbar rantsuwar aiki na wani wa’adin shekaru 5 akan madafan iko, inda ya lashi takobin bude wa kasar wani sabon babi a dangantakarta da sauran kasashen duniya.

Omar Hassan al-Bashir Shugaban kasar Sudan
Omar Hassan al-Bashir Shugaban kasar Sudan Reuters/Mohamed Nureldin Abdallah
Talla

Omar Hassan al Bashir ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar da kusan kashi 94, inda zai sake shafe wasu shekaru biyar yana jagorantar kasar.

Al Bashir ya sake lashe zaben Sudan duk da zarginsa da kotun ICC ke yi da aikata laifukan yaki, yayin da kuma ya ke ci gaba da fuskantar suka daga kasashen yammaci.
Kasashen yammaci da dama dai sun soki zaben, musamman kungiyar Tarayyar Turai da Amurka da Birtaniya da Norway.

Amma masu sharhi na ganin mutanen Sudan sun gamsu da shugabancin al Bashir shi ya sanya suka sake zabensa duk da wasu ‘Yan adawa sun kauracewa zaben.

Kalubalen da ke gaban al Bashir a yanzu shi ne farfado da tattalin arzikin kasar tare da kawo karshen rikici a yankin Darfur da Blue Nile da kudancin Kordufan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.