Isa ga babban shafi
Burundi

Shugabannin Gabashin Afirka sun bukaci a dage zaben Burundi

Shuwagabannin kasashen yankin gabashin Afrika da suka gudanar da wani zaman taro a yau lahadi a Dar As Salam na kasar Tanzaniya, kan rikicin kasar Brundi sun bukaci daga gudanar da zaben shugabancin kasar da wata guda da rabi nan gaba, zabe da ya kamata a ce an gudanar da shi a ranar juma a mai zuwa.

Wani mai zanga-zanga dauke da allon da ke yin kira a kawo karshen mulkin Nkurunziza
Wani mai zanga-zanga dauke da allon da ke yin kira a kawo karshen mulkin Nkurunziza REUTERS/Goran Tomasevic
Talla

Haka kuma shugabanin sun yi kiran da a kwantar da hanakali a kasar.

Makwanni biyu da suka gabata shugabannin kasashen yankin na Gabashin Afirka sun gudanar da tarao makamancin wannan, kuma a lokacin ne wasu sojoji suka yi yunkurin kifar da gwmanatin shugaba Nkurunziza.

A ranar asabar ministocin harkokin wajen kasashen Ruwanda, Burundi, Uganda, Kenya da kuma Tanzania, sun gudanar da taron share fage kan wannan batu.

To sai dai fadar shugaba Pierre Nkurunziza ta tabbatar a cewa shugaban ba zai halarci taron na yau ba.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.