Isa ga babban shafi
Najeriya

Jonathan ya bukaci gaffara 'yan Najeriya

Shugaban Najeriya mai barin gado Goodluck Jonathan ya bukaci 'yan kasar da su yafewa kura kuran da gwamnatin  sa ta aikata, lokacin gudanar da aikace aikacen ta. Yayin da ya ke jawabi shugaban ya ce akwai wasu matakai da suka dauka wadanda inda yanzu ne da basu dauke su ta wadancan hanyoyin ba. 

Shugaba Goodluck Jonathan mai barin gado
Shugaba Goodluck Jonathan mai barin gado rfi hausa
Talla

Sai ya kara da cewar wasu matakan ba wai an dauke su ne dan a batawa wasu jama'a ba sai dai dan yanayin da shugabanni suka samu kan su a wancan lokacin. Jonathan yace a shirye yake ya ci gaba da yiwa jama'a hidima a matakai dabam dabam ba wai sai a mukamin gwamnati ba.

Jonathan ya yi wannan roko ne a jawabinsa lokacin wasu addu’o’i na bankwana da aka shirya a wata mujami’a da ke cikin fadar sa, inda a lokacin aka mika cocin a hannun wakilan mataikamin shugaban kasa mai jiran gado Farfesa Yemi Osinbajo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.