Isa ga babban shafi
Najeriya

Yara 150 sun gagara zuwa makaranta a Zamfara

Kungiyar agaji ta Save the Children dake tallafawa yara kanana, ta koka kan yadda kashe kashen da aka yi kauyen Yar’Galadima dake Jihar Zafara a arewacin Nigeria, cikin watan Aprilun bara yayi sanadiyyar yara da dama suka gagara ci gaba da makatanta.

Yara suna koyon hura mabusar Gwanda
Yara suna koyon hura mabusar Gwanda UNESCO
Talla

Wani rahoton da kungiyar ta fitar, yayin da ake cika shekara guda da harin, inda aka hallaka kusan mutane 200 a kauyen Yar’Galadima, kungiyar ta ce akalla yara 150 sun fice daga makatranta saboda ba sa iya biyan kundin tallafi, na Naira 100 da ake bayarwa duk wata, a matsayin tallafi don tafiyar da makarantar da ke kauyen.

Kungiyar ta Save the Children ta ce tsananin talauci yasa iyaye da masu kula da wadanan yaran janye su daga makarantar Frimare.

Kungiyar ta rawaito wasu daga cikin magidanta a kauyen suna cewa ba su da zabi face su janye ‘ya ‘yan na su daga makarantar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.