Isa ga babban shafi
Cote D'Ivoire

Ba a kwace makaman Tsoffin ‘yan tawayen Cote d’Ivoire ba

Wani Bincike ya nuna cewar har yanzu wasu ‘yan tawayen kasar Cote d’Ivoire da suka taimakawa shugaba Alassane Ouattara ya karbi mulki a shekarar 2011 har yanzu suna rike da makamansu a barikin soji. Binciken ya ce mayakan na bukatar ganin an sanya su cikin aikin soja ko a sallame su da kudade domin su kama gabansu.

Shugaban kasar Cote d'Ivoire Alassane Ouattara
Shugaban kasar Cote d'Ivoire Alassane Ouattara Montage/RFI
Talla

Sai dai kuma shugaban kasar Alassane Ouattara ya shaida musu cewar ya zuwa yanzu babu wani gurbin daukar mutane a rundunar sojin kasar, bayan an dauki 13,000 tare da umurtar su fice daga barikin soji nan da karshen watan Yuni mai zuwa,

Shugaban kuma ya bukaci ‘yan tawayen su mika makamansu.

Ana fargabar cewar kyale ‘Yan tawayen haka nan na iya sa ‘yan siyasa su yi amfani da su wajen zaben kasar da za a yi nan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.