Isa ga babban shafi
Chibok

Shekara guda da sace ‘Yan Matan Chibok

A yau Talata 14 ga watan Fabrairu aka cika shekara guda da mayakan Boko Haram suka sace ‘Yan mata Daliban Makaranta su 276 a garin Chibok Jihar Borno arewacin Najeriya. Kungiyoyi na ci gaba da kira ga mahukuntan Najeriya da kasashen duniya su kara daukar matakai domin ganin an kubutar da Daliban.

'Yan Matan Chibok da aka sace a  cikin wani hoton bidiyo da Mayakan Boko Haram suka wallafa
'Yan Matan Chibok da aka sace a cikin wani hoton bidiyo da Mayakan Boko Haram suka wallafa AFP/via telegraph
Talla

Bikin juyayin, na zuwa ne a yayin da Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta wallafa rahoto da ke cewa akalla mata 2,000 kungiyar Boko Haram ta sace a Najeriya tun farkon shekarar da ta gabata.

A yau kungiyoyi da dama za su hada gangami a Abuja babban birnin Tarayyar Najeriya domin yin kira ga hukumomin kasar su gaggauta kubutar da ‘Yan matan.

A ranar 14 ga watan Fabrairun bara ne mayakan Boko Haram suka abka wa makarantar mata a garin Chibok cikin Jihar Borno suka sace ‘Yan mata 276 a lokacin da suke shirin rubuta jarabawa.

57 daga cikin matan sun tsere amma har yanzu babu wani labari akan sauran ‘yan matan.

Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ya fito a wani faifan bidiyo yana ikirarin cewa ya aurar da dukkanin matan tare da musuluntar da su.

Kungiyar Amnesty tace mayakan Boko Haram suna lalata da wasu ‘yan matan, tare da tursasa mu su daukar makamai.

An dade rundunar Sojin Najeriya na ikirarin cewa ta san inda ake garkuwa da ‘Yan matan Chibok, amma tana fargaba akan tsoron kada a kashe su wajen kubutar da su.

Batun sace ‘Yan matan dai na daya daga cikin dalilan da suka janyo wa gwamnatin Goodluck Jonathan bakin jini a Najeriya, inda ya sha kaye a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 28 ga watan Maris.

Amma Shugaban Najeriya mai jiran gado Janar Muhammadu Buhari ya ce ba zai yi alkawalin kubutar da ‘Yan Matan Chibok 219 ba da Boko Haram ta sace saboda har yanzu ba a san inda ake garkuwa da su ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.