Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 11/11 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 10/11 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 10/11 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 11/11 06h17 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 10/11 07h00 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 11/11 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 10/11 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 11/11 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 10/11 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 11/11 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 10/11 16h06 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 11/11 16h30 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 10/11 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 10/11 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 11/11 16h40 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 10/11 20h00 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 11/11 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 10/11 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 11/11 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Afrika

Ana zaman makokin daliban Jami'a da aka kashe a kasar Kenya

media Jama'a suna addu'a ga daliban da aka kashe a Jami'ar Garissa ta kasar Kenya RFI/Sonia Rolley

An fara zaman makoki na tsawon kwanaki uku daga jiya lahadi a kasar Kenya, bayan mumunan harin ta’adanci da kuniyar al-shabab ta kai, tare da kashe mutane kusan mutane 150 a Jami’ar Garissa da ke gabashin kasar. Tun daga jiya lahadi majami'u kasar ke yin addu'o'i na musamman ga daliban da mayakan al-Shabab suka kashe, a harin mamayar da Kungiyar ta kai wa Jami’ar, tsawo Sa’o’i 15.
Kuma kamar yadda bayanai suka nuna, Mayakan na al-Shabab sun kashe daliban ne akan dalilai na addini, lura da yadda suka rika ware wadanda ba Musulmi ba kafin su kashe su.
Yayin addu’o’in da ya gabatar dangane da zagayowar ranar Easther Shugaban mujami’an Anglican a kasar ta Kenya, Archbishop Eliud Wabukala yayi Allawadai da harin, inda ya ce za su ci gaba da yin addu’i’o tare da neman tsari daga irin wannan mumunar harin a nan gaba.
Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya ce kasar za ta dauki fansa dangane da wannan hari, amma ba tare da an cutar da musulmin kasar marasa rinjaye wajen daukar fansar ba, sannan kuma ya bukaci samun hadin kai a tsakanin al’ummar kasar baki daya.
Shugaba Kenyatta ya bukaci al’ummar musulmin Kenya, da ya ce suna da halayen kirki, da su taimaka a gano sauran wadanda ke da hannu wajen aiwatar da wannan danyen aiki.

Wannan dai shine hari mafi muni da aka kai wa kasar ta Kenya, tun bayan wanda aka kai a ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Nairobi a 1998, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane masu tarin yawa a wancan lokacin.
 

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure