Isa ga babban shafi
Sudan

Boko Haram: Al Bashir ya zargi Amurka da Isra’ila

Shugaban Kasar Sudan Omar Hassan al Bashir ya yi zargin cewar CIA ta Amurka da Mossad ta Isra’ila na da alaka da kungiyoyin IS da Boko Haram da ke da’awar Jihadi a duniya. Al Bashir ya fadi haka ne a wata hira da ya yi da tashar Euronews da za’a nuna yau laraba.

Shugaban Sudan Omar Hassan Al Bashir
Shugaban Sudan Omar Hassan Al Bashir Reuters
Talla

Al Bashir ya ce babu yadda za a yi Musulmi ya dauki bidiyo yana fille kan jama’ar da ba su ji basu gani ba, bayan Mayakan IS sun yi wa wasu Kiristocin Masar yankar rago a wani bidiyo da suka nuna a Intanet.

Shugaban na Sudan ya ce idan ana neman zaman lafiya ya dace a zauna teburin sulhu da Mayakan maimakon daukar matakin Soja akansu.

Al Bashir ya ce abkawa Mayakan mataki ne da zai dada haifar da wasu masu tsautsaran ra’ayi a duniya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.