Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Mandela ya cika shekara guda da mutuwa

A yau Juma’a 05 ga watan December ne, tsahon shugaban kasar Afrika ta kudu dottijo Nelson Mandela ya cika shekara guda da mutuwa, mutumen da daukacin kasashen duniya ke girmamawa, sakamakon dattakonsa, da kuma gwagarmayar da ya yi na yaki da mulkin wariyar launin fata (apartheid) a kasar

shagulgulan cikar mandela shekara guda da mutuwa
shagulgulan cikar mandela shekara guda da mutuwa REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

shekara guda kenan da katafariyar kasar nan mai launinin bakan gizo, da ta hada bakake da fararen fata Afrika ta kudu ta rasa gwarzon danta, dattijo nalson Mandela da ya bar duniya yana dan shekaru 95 , mutumin da ya kasance abin koyi ga nahiyar da ma duniya baki daya.

Halayen dattako, yafiya tare hada kanun al’ummar kasar da ya yi, bayan tsawon shekaru kasar na karkashin mulkin turawa na wariyar launin fata.

Bikin tunawa da wannan gwarzo abin koyi, ya cika shekara guda da komawa ga mahalicinsa, na gudana ne, da yi masa addu’oin neman afuwar ubangiji da gwamnatin kasar ta shirya, hade jawaban yabawa da kokarin da ya yi wajen yantar da miliyoyin bakaken fatar kasar, daga karkashin mulkin mulaka’un turawa, jawaban da suka kwadaitar da al’umma, koyi da irin wadannan halaye nasa, musaman wajen nuna yafiya, tare da watsi da tsarin ramuwar gayya da ya nuna, a lokacin, da ya share tsawon shekaru 27 a gida yari,

Ron Martin shugaban yan kabilar Khoisan (bushman), kabilar da aka yi ittifakin cewa itace ta farko a wannan yanki da ake kira kasar Afrika ta kudu, shine ya kaddamar da soma addu’oin, ya ce, tsarin mulkin demokradiyar tsawon shekaru 20 da suka samu a kasar, na faruwa ne alfarmar Nelson Mandela".

Inda ya kara da cewa, a baya a karkashin mulkin wariyar launin fatar, duk wani fata na gari hade da kwanciyar hankali bai samu gurbin zama baa garesu, to’ amma a yau sun yi nasarar sake maido da hakki, martaba da diyaucin da suka rasa tsawon shekaru

Ron Martin ya yaba tare da jinjinawa Mandela, kafin ya kona wasu ganyayyaki a ani kahon Barewa bisa tsarinsu na Al’ada, wanda kuma hakan ne, ya buda soma gudanar da addu’oin daga mabiya addinai daban daban na kasar, da suka hada da na Kristanci, Hindu, Musulunci, yahudanci, da ma na yan rastafari
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.