Isa ga babban shafi
Najeriya

Gidauniyar Elumelu za ta bunkasa kasuwanci a Afrika

Gidauniyar Hamshakin attaijirin Najeriya, Tony Elumelu ta sanar da bayar da gudumawar Dala miliyan dari don bunkasa kasuwancin matasa a Nahiyar Afrika. Attajirin ya bayar da gudumawar Dala miliyan 100 don bunkasa harkokin kasuwancin matasa a nahiyar Afrika.

Gidauniyar Hamshakin attaijirin Najeriya, Tony Elumelu
Gidauniyar Hamshakin attaijirin Najeriya, Tony Elumelu connectnigeria.com
Talla

Shirin zai shafi tallafawa matasa 10,000 daga nahiyar Afrika don ganin sun kafa kasuwanci mai dorewa da zai sa su tsaya da kafafuwansu, da kuma ganin sun tallafawa nahiyar.

Attajirin yace idan bai yi haka ba, Allah ba zai yafe masa ba ganin yadda ya amfana da nahiyar da kuma dunkiyar da ya tara.

Ya kara da cewar bukatar sa shi ne ganin matasa 10,000 daga nahiyar Afrika sun kafa harkokin kasuwanci na kansu inda cikin shekaru 10 za a samu ayyuka sama da miliyan guda.

Elumelu ya bayyana cewar za a dauki matasan ne daga kasashe 54 na Afrika, kuma duk wanda ya samu shiga zai samu Dala 10.000.

Jami’ar da ke kula da shitrin, Parminder Vir, tace babu addadin shekarun da aka kebe na masu shiga shirin,

Ana sa rana shirin ya fara aiki daga farkon shekarar 2015.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.