Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya ta rage darajar Naira

Babban Bankin Najeriya CBN ya rage darajar kudin Naira bisa dalilan faduwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya. Gwamnan babban bankin Godwin Emefiele yace tuni darajar kudin ta fadi a cikin gida kafin daukar wannan matakin.

Kudin Naira na Najeriya
Kudin Naira na Najeriya Juguda.com
Talla

Babban Bankin ya ce ana cinikin Naira akan farashi 180 akan dalar Amurka, sabanin farashin gwamnati 150 zuwa 160.

Najeriya da ke dogaro da arzikin fetir tana kokarin daukar matakan kare darajar kudinta ne saboda faduwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya.

Yanzu Babban Bankin ya tsayar da farashin dalar Amurka daidai ta Naira 168, tare da kara kudaden ruwa daga kashi 12 zuwa 13.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.