Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Sojoji za su amince da mika mulki ga farar Hula a Burkina Faso

Shugaban kasar Senegal, Macky Sall ya bayyana yakini cewar, sojin kasar Burkinafaso hade da kungiyoyin fararen hula za su amince da tsarin da aka fitar na mika mulki ga farar Hula bayan kifewar shugabancin Blaise Campore da ya mulka kasar har tsawon shekaru 27

Zéphirin Diabré, kiongozi wa upinzani, mbele ya vyombo vya habari, baada ya mkutano na wawakilishi wa vyama vya kiraia, viongozi wa kidini na kimila, Ougadougou, Novemba 11 mwaka 2014.
Zéphirin Diabré, kiongozi wa upinzani, mbele ya vyombo vya habari, baada ya mkutano na wawakilishi wa vyama vya kiraia, viongozi wa kidini na kimila, Ougadougou, Novemba 11 mwaka 2014. ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Shugaban kasar ta Senegal, wanda kuma jakada ne na kungiyar kasashen yammacin Afrika, ya ziyarci birnin Ouagadougou domin bada gudun-mawa bisa yadda mulkin kasar Burkina faso zai koma hannun farar Hula a saukake.

Kamar yadda Macky Sall ya shedawa manema labarai, yanada tabbacin cewa, sojin kasar za su bada cikken hadin kai wajan sa hannu domin nuna amincewarsu da tsarin mika mulki ga farar Hula a kasar ta Burkinafaso.

Yanzu dai kungiyoyin fararen hula sun amince da a gudanar da zaben nan da shekara daya, sabanin makonni biyu da aka nema a farko.

Tsarin yarjejeniyar dai, ya nuna za'a gudanar da zaben a cikin watan Nuwamban shekara mai zuwa yayin da har yanzu ba’a tsayar da farar Hulan da zai rike mulkin kasar ba kafin zaben.

Sojin dai da suka karbi mulki daga hannun Blaise Campore, na samun matsin lamba daga kasashen duniya da suka hada da kungiyar nahiyar turai, da su gaggauta gudanar da sabon zabe da zai baiwa fararen Hula damar rike kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.