Isa ga babban shafi
Gates

Gidauniyar Bill Gates ba ta isa ga Talakawa

Wani Bincike ya nuna cewar akasarin tallafin da Gidauniyar Bill Gates ke bayar wa don bunkasa ayyukan noma a kasashe matalauta yana tafiya ne ga kungiyoyin agajin da ke kasashen da suka ci gaba. Binciken ya nuna cewar kashi 80 na sama da Dala biliyan uku da Gidauniyar ke bayarwa a cikin shekaru 10 sun tafi ne ga Bankin Duniya, da kuma kungiyoyin da ke Amurka da Britaniya da Jamus da kasar Holland, yayin da kashi 10 kacal ke zuwa Afrika.

Bill Gates da Melinda Shugabannin gidauniyar Gates.
Bill Gates da Melinda Shugabannin gidauniyar Gates. REUTERS/Rick Wilking
Talla

Binciken yace kashi 10 kuma babu wanda ya san inda ake karkatar da su. Binciken yace tallafin ba ya amfanar wadanda ake bayar wa domin su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.